Iran Ta Jinjina Wa Matsayar Da Pakistan Ta Dauka Akan Harin Da HKI Ta Kawo Wa Iran

Janar Abdurrahim Musawi wanda ya tattauna ta wayar tarho ta kwamandan sojojin jamhuriyar  musulunci ta Pakistan, Asim Munir, ya yi jinjina akan mataki na jarunta

Janar Abdurrahim Musawi wanda ya tattauna ta wayar tarho ta kwamandan sojojin jamhuriyar  musulunci ta Pakistan, Asim Munir, ya yi jinjina akan mataki na jarunta da Pakistan din ta dauka akan harin da HKI ta kawo wa Iran, haka nan kuma yadda ta nuna goyon bayanta ga Iran.

Janar Musawi ya  kuma yi ishara da matsayar gwamnati da al’ummar Pakistan akan ta’addanci na HKI, kamar kuma yadda ya bayyawa kwamandan sojojin kasar ta Pakistan yadda Amurka ta taimakawa HKI a tsawon kwanaki 12 na yakin.

 Har ila yau, janar Musawi ya ce; Tare da cewa mun rasa kwamandoji masu girma a farkon harin ta’addancin, sai dai kuma duk da haka, mun hana ‘yan sahayoniyar cimma manufofinsu.

A farkon yakin dai, kasar Pakistan ta bakin shugabanninta sun yi tir da harin na HKI, tare da nuna cikakken goyon bayansu ga jamhuriyar musulunci ta Iran wacce su ka bayyana a matsayin ‘yar’uwa kuma makwabciya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted