Iran Ta Ja Kunnen Kasashen Turai Da Amurka Kan Amfani Da Damar ‘Snapback’ Kan Shirin Nukliyarta

Jakadan kasar Iran a MDD Amir Sa’eid Iravani ya kara jaddadawa kasashen turai 3 da Amurka dangane da hatsarin anfani da damar ‘Snapback’ a cikin

Jakadan kasar Iran a MDD Amir Sa’eid Iravani ya kara jaddadawa kasashen turai 3 da Amurka dangane da hatsarin anfani da damar ‘Snapback’ a cikin yarjeniyar nukliya ta kasar Iran da kuma kudurin mai lamba 2231. Ya kuma bukacesu su dawo kan hanyar tattaunawa don warware matsalolin da suke gani tattare da shirin makamashin nukliya na kasar Iran.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a gaban kwamitin tsaro na MDD inda kasashen uku na turai wato Jamus, Ingila da faransa, tare da Amurka suka kawo batun amfani da damar ‘Snaback’ ta maida dukkan takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa JMI a shirinta na makamacin nukliya, don cimma manufofinsu na siyasa.

Jakadan ya ce, idan wadannan kasashen suna son gaskiya da zaman lafiya to su hana HKI abinda take yi a yanking abas ta tsakiya. Amma ba rufe idanunsu zasu yi a kan ta’asanda HKI take aikatawa a Gaza ba. Yace yiwa Iran barazana, maido da takunkuman tattalin arzikin da kuduri mai lamba 2231 ya bada damar yin hakan ba zai tainakawa al-amura ba.

Daga karshe jakadan ya kammala da cewa idan wadannan kasashe sun dauki wannan tafarkin, to, abin ba zai yiwa kowa dadi ba. Don Iran zata maida martani da abinda ya yi dai-dai da abinda suka yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments