Iran Ta Gayyaci Jakadun Kasashen Turai Kan Matakin Da kungiyar EU Ta Dauka Kan IRGC

Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta gayyaci jakadun kasashen Turai domin nuna rashin jin dadinta game da matakin da kungiyar tarayyar turai ta dauka na

Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta gayyaci jakadun kasashen Turai domin nuna rashin jin dadinta game da matakin da kungiyar tarayyar turai ta dauka na sanya sunan dakarun kare juyin musulunci na iran a jerin sunayen kungiyoyin yan taadda,

jakadun, mataimakin ministan harkokin wajen kasar iran kan harkokin siyasa, da kuma manyan daraktocin da abin ya shafa ne suka gayyacesu, inda iran ta nuna rashin amincewarta da mataken da tarayyar turai ta dauka, a wata sanarwa da Ma’aikatar harkokin waje ta fitar

A ranar Alhamis da ta gabata ce ministocin kasashen kungiyar tarayyar Turai suka sanar da yarjejeniyar da suka cimma matsaya akai, na sanya sunan kungiyar IRGC a cikin jerin sunayen kungiyoyin da suka kira a matsayin yan ta’adda, yayin da gwamnatin iran ta dade tana bayyana irin rawar da  kungiyar ta taka wajen murkushe kungiyoyin yan ta’adda a yanki.

a lokacin ganawar ta su da jami’an diplomasiyar kungiyar tarayyar Turai, ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta yi tir da matakin da kungiyar tarayyar turai ta dauka na rashin adalci kuma ta bayyana shi a matsayin take dokokin kasa da kasa ne.da rashin mutunta kasar da tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted