Kasar Iran ta gayyaci jakadan kasar Saudiyya a birnin Tehran domin nuna kakkausan bakin ran ta kan hukuncin kisan da Masarautar ta zartar kan wasu ‘yan kasar Iran din guda shida da aka daure a gidan yari a kasar bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.
Iran ta mika da jakdan kakkausan bacin ran kan matakin wanda ta ce ba abinda za’a lamunta da shi ne ba, hasali ma ya sabawa dokokin kasa da kasa kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanar.
Iran ta shaidawa jakadan na Saudiyya cewa hukuncin kisa bai dace da yanayin hadin gwiwar shari’a a tsakanin kasashen biyu ba.
“Mahukuntan Saudiyya sun yanke wa wadannan mutane hukuncin kisa shekaru da dama da suka gabata kan zargin safarar miyagun kwayoyi.
Aiwatar da hukuncin kisan ba tare da sanar da ofishin jakadancin Iran “ba abu ne da ba za a amince da shi ba” kuma ya saba wa ka’idojin shari’a na kasa da kasa, ciki har da yarjejeniyar Vienna kan huldar jakadanci, in ji ma’aikatar harkokin wajen Iran.
Sanarwar ta ce, wata tawaga ta ma’aikatar kula da harkokin waje ta bangaren shari’a da ta jakadanci za ta je Riyadh domin bin diddigin lamarin.
Wani rahoton da wata Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Turai (ESOHR) ta fitar a shekarar da ta gabata, ya ce akalla mutane 1,243 ne aka kashe a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2021 a kasar Saudiyya, lamarin da ya sa masarautar Larabawa ta kasance a jerin kasashen da suka fi fuskantar hukuncin kisa a duniya.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa sun jaddada cewa ba a san hakikanin adadin mutanen da ake kashewa a kasar ba saboda mahukuntan Saudiyya ba su bayar da wani bayani kan shari’ar manyan laifuka.