Kani: Iran tana kan bakanta na bin matakan shari’a kan batun kisan Janar Soleimani

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa kasar za ta yi watsi da duk wani yunkuri na neman ta dakatar da batun bin kadun

Mukaddashin ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa kasar za ta yi watsi da duk wani yunkuri na neman ta dakatar da batun bin kadun kisan Kasim Sulaimani ta hanyoyi na shari’a.

Ali Bagheri Kani ya bayyana hakan ne ga wakilin CNN Fareed Zakaria a ranar Laraba a birnin New York, inda babban jami’in diflomasiyyar ya je domin halartar tarukan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya guda biyu.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an yi adalci a cikin lamarin, yana mai mai cewa, “Wannan hakkinmu ne.”

Laftanar Janar Qassem Soleimani, kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) da Abu Mahdi al-Muhandis, mataimakin babban kwamandan rundunar masu fafutuka na Iraki (PMU), an kashe su tare da abokan tafiyarsu a wani hari da jirgin Amurka maras matuki ya kai kansu a cikin kasar Iraki.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ne da kansa ya bayar da umarnin kai harin a kusa da filin jirgin sama na Baghdad a ranar 3 ga Janairu, 2020.

Kwamandojin sun samu karbuwa sosai a fadin yammacin Asiya saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen yakar kungiyar ta’addanci ta Daesh a yankin, musamman a Iraki da makwabciyarta Syria.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments