Iran Ta Ce, HKI Zata Fada Cikin Jahannama Idan Ta Yi Kokarin Mamayar Kasar Lebanon

Mukaddashin ministan harkokin wajen JMI Ali Bakiri Kani ya bayyana cewa, HKI zata jefa kanta cikin Jahannam idan ta kuskura ta farwa kasar Lebanon da

Mukaddashin ministan harkokin wajen JMI Ali Bakiri Kani ya bayyana cewa, HKI zata jefa kanta cikin Jahannam idan ta kuskura ta farwa kasar Lebanon da yaki da nufin mamayarta.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Bakiri Kani yana fadar haka a lokacinda yake jawabin hadin giwa da Qasim Al-Araji mai bawa firaiministan kasar Iraki shawara a kan harkokin tsaro a birnin Bagdaza a jiya Alhamis.

Kani ya kara da cewa al-amura sun sauya tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata, a lokacinda dakarun Hamas suka yi wa HKI ba zata a matsugunan yahudawan da suke gewaye da yankin.

Tun shekara ta 2000 ne sojojin HKI suke shan kaye a hannun dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon bayan sun mamaye kasar a shekara 1982.

Da farko dakarun kungiyar sun kori sojojin HKI daga kasar Lebanon a shekara ta 2000, sannan a lokacinda suke son sake mamayar kasar a shekara ta 2006 ma, dakarun hizbullah sun fatattakesu.

A halin yanzu dai tun ranar 8 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ce, bangarorin biyu suke musayar wuta a tsakaninsu a kudancin kasar Lebanon da kuma arewacin HKI.

Amma a jiya Alhamis dakarun kungiyar Hizbullah sun maida martini mai tsanani kan HKI bayan da sojojin yahudawan  suka kashe wani babban kwamandan kungiyar a garin Juwayya dake kudancin kasar ta Lebanon.

A wani labarin kuma tashar talabijin ta 12 ta HKI ta nakalto Benny Gantz wani dan majalisar dokokin HKI ‘Knesset´ya na cewa dole ne gwamnatin HKI ta kona kasar Lebanon saboda hare haren da ta kai kan arewacin kasar.

Ganz dai ya fice daga gwamnatin Natanyahu, saboda abinda ya kira rashin wani shirin da gwamnatin Natanyahu ta yi bayan yaki a Gaza, amma yace yana goyon bayan gwamnatin Natanyaho ta kona kasar Lebanon.

Kungiyar Hizbullah dai ta sha alwashin ci gaba da kai hare hare kan cibiyoyin tsaro na HKI matukar ta ci gaba da kissan kare dangi a Gaza.

Ya zuwa yanzu dai sojojin yahudwan sun kashe falasdinawa kimani dubu 40 a gaza, a yayinda wasu kimani dubu 85 suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments