Iran Ta Ce: Babu Tattaunawa Da Amurka Har Sai Amurka Ta Dawo Cikin Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Ita  

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Babu zatattaunawa da Amurka matukar ba ta dawo kan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma a baya da

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Babu zatattaunawa da Amurka matukar ba ta dawo kan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma a baya da Iran ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Manufar Iran a halin yanzu ba ita ce ta gudanar da zaman tattaunawa da Amurka ba, sai dai idan sun koma kan yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a baya, yana mai jaddada cewa, cikakken yarjejeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Rasha ba ta sabawa wani bangare na uku ba.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar a wata hira da gidan talabijin na kasar Iran a yammacin jiya Talata cewa: Iran za ta rattaba hannu kan cikakkiyar yarjejeniya da kasar Rasha a ziyarar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai kai birnin Moscow a ranar Juma’a mai zuwa.

Ya bayyana cewa: Yarjejeniyar ta kunshi dukkan bangarorin tattalin arziki, kasuwanci, majalisar dokoki, tsaro da hadin gwiwar soji, yana mai jaddada cewa ba hadin kai ba ne na sojoji don wasu dalilai na musamman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments