Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi kira da a samar da wani sabon mataki na fahimtar juna da hadin gwiwa tsakanin Iran da kungiyar hadin kan yankin tekun Fasha (GCC).
Yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na GCC Jassim Mohammed al-Budaiwi, Araghchi ya jaddada cewa Iran na da sha’awar inganta alakar ‘yan uwantaka da kasashe mambobin kungiyar.
Ya kamata alakar Iran da GCC ta shiga wani sabon yanayi na fahimtar juna da hadin gwiwa, in ji ministan harkokin wajen Iran.
A nasa bangaren, al-Budaiwi ya taya Araghchi murnar nadin da aka yi masa a matsayin sabon ministan harkokin wajen kasar Iran tare da tattauna hanyoyin karfafa alaka tsakanin Tehran da kungiyar.
Da yake jaddada cewa Iran na taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, al-Budaiwi ya ce kasashen GCC na da sha’awar tuntubar Iran kan manyan kalubalen da ke fuskantar yankin.
Wannan dai na da daga cikin alkawuran da Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran ya dauka na cewa gwamnatinsa za ta ba da fifiko wajen karfafa alaka da makwabta.