Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a ke Geneva, Ali Bahraini ya gabatar da jawabi ga taron hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD karo na 56 wanda aka gudanar a birnin Ganeva, inda ya wakilci kasashe da dama don bayyana HKI a matsayin kasar mai nuna wariya.
Bahraini ya bukaci a sake farfado da kurdurin babban zauren MDD mai lamba 3379 ta shekara 2017. Wanda kafin a samar da kudurin hukumar UNESCO ta gabatar da rahoton cewa HKI tana mu’amala da Falasdiawa kamar yadda tsarin wariya take.
Jakadan ya kara da cewa aiwatar da tsarin wariyan da HKI take yi, keta hukumin kudurorin MDD da dama ne, sannan sun sabawa yarjeniyoyin kas da kasa da dama.
Daga karshen jakadan wanda yayi magana a madadin kasashen musulmi da kuma wasu kasashen da suke kawance da su, ya bukaci kasashen duniya su shelanta HKI a matsayin kasa mai nuna wariyar a duniya, saboda yadda take mu’amala da Falasdinawa a kasarsu da ta mamaye fiye da shekaro 76 da suka gabata.