A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Holland, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da ci gaba da mamaya da kuma laifukan da yahudawan sahayoniyya suke yi a Falasdinu, tare da yin kira ga kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa wajen hanzarta bibiyar bayanan shari’a da laifuka a kotunan duniya dangane da kisan kiyashi da laifukan yaki da shugabannin mamayar Isra’ila suka aikata.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya habarta cewa: Ministan harkokin wajen kasar Holand Caspar Veldkamp da takwaransa na Iran Abbas Araqchi sun tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu da ci gaban kasa da kasa a wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho a jiya Asabar.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da dogon tarihin dangantakar da ke tsakanin Iran da Netherlands, ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye ta ke ta gudanar da dukkanin harkokin da suka shafi kasashen biyu bisa mutunta juna da moriyarsu.