Iran Ta Baiwa Ma’aikatan Hukumar IAEA 100 Izinin Yin Aiki A Kasar

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) ya ce a wani mataki na hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyar Musulunci da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) ya ce a wani mataki na hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyar Musulunci da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), kasar, ta baiwa ma’aiakta na hukumar IAEA sama da 100 izinin yin aiki a kasar.

“Ba mu hana wani jami’in hukumar IAEA zuwa Iran ba. Kimanin jami’an hukumar IAEA 130 ne aka ba su izinin ziyartar Iran da gudanar da bincike,” kamar yadda, Mohammad Eslami ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin kasar na ranar Laraba.

Ya bayyana yadda ake ci gaba da tuntubar juna da tattaunawa tsakanin Iran da hukumar nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya karkashin yarjejeniyar kare kai (CSA), yana mai cewa, yayin da aka kammala tattaunawa kan batutuwan da suka shafi wasu wurare guda hudu da ake zargin ba a bayyana a Iran ba, ya ce an kammala tattaunawa kan wurare biyu.

Wannna furicin na shugaban hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Duniya Rafael Grossi, zai ziyarci Iran a makon gobe, kamar yadda MDD, ta sanar a jiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments