Search
Close this search box.

Iran: Shugaban Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya Ya Isa Birnin Tehran Don Ziyarar Aiki

Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta Duniya Rafael Grossi ya isa birnin Tehran a safiyar yau tare da tawagarsa, don halattan taron kasa da kasa ta

Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta Duniya Rafael Grossi ya isa birnin Tehran a safiyar yau tare da tawagarsa, don halattan taron kasa da kasa ta makamashin nukliya wanda za’a gudanar a birnin Esfahan na tsakiyar kasar

Kamfanin dillancin labaran Isna na kasar Iran ya bayyana cewa Grossi zai gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Hussain Abdullahiyan a yau Litinin, sannan zai wuce birnin Esfahan inda zai halarci taron kasa da kasa na farkon kan makamashin nuikliya a nan Iran. Inda kuma ake saran zai gana da shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran Muhammad Islami, sannan ya amsa tambayoyin yan jarida dangane da al-amuran makamashin nukliya a duniya, musamman a kasar Iran.

Labarin ya kara da cewa bayan gudanar da tarurruka na makamashin nukliya a cikin kasa har sau 29, a wannan karon Iran zata gudanar da taron kasa da kasa kan fasahar nukliya a fagen kasa da kasa. Kuma ya zuwa yanzu masana kimani 50 daga kasashen duniya daban daban ne suka gabatar da bayanan da suke bukatar a tattaunasu a wannan taron. Za’a bude taron a yau litinin, sannan a kamala shi a ranar Laraba 8 ga watan Matun da muke ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments