Iran: Shugaba Pezeshkiyan Ya Ziyarci Dangin Shahidi Kirista A Yakin Shekaru 8

A dai dai lokacinda mabiyan addinin kirista a duk fadin duniya suke bukukuwan haihuwar annabi Isa (a) shugaban kasar iran Masoud Pezeshkiyan ya ziyarci dangin

A dai dai lokacinda mabiyan addinin kirista a duk fadin duniya suke bukukuwan haihuwar annabi Isa (a) shugaban kasar iran Masoud Pezeshkiyan ya ziyarci dangin daya daga cikin shahidai kiristoci a yakin mai tsarki na shekaru 8 mai suna Razmik Khachatorian a nan Tehran.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa shugaban ya sami rakiyar Ara Shahverdyan dan majalisar dokokin kasar Iran mai wakiltan mabiya addinin kirista a nan Iran. Ya kuma gabatar ta gaisuwarsa ga dangin shahidin saboda zagayowar ranar haihuwar annabi Isa (a) da kuma sabuwar shekara mai zuwa.

A ziyarar a jiya Alhamis 25 ga watan Decemba ga iyalan shahidin shugaban ya gabatar da ta’aziyyarsa ga iyalan kan rashin Khachatorian da kuma hakurin da suke ci gaba da yi na shahadarsa. Ya ce shahadarsa wajen kare JMI wata alamace ta hadin kan mutanen kasar Iran daga dukkan mabiyan addinai daban-daban na kasar.

Shugaban ya kammala da cewa karfin da JMI take da shi a halin yanzu ya samo asali ne daga sadaukarwan da shahidan kasar suka yi a yakar makiyan kasar kama daga yakin shekaru 8 da kuma na kwanaki 12. A nasu bangaren iyalan gidan Khachatorian tare da Ara Shahverdyan, wakilin kiristoci a Majalisar dokokin kasar Iran sun godewa shugaban kasar kan ziyarar da ya kawo masu, sun kuma kara jaddaba biyayyasu ga tsarin da manofofin JMI da kuma tafarkin shahidan kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted