Tun da misalin karfe 10;00 safiyar yau Juma’a ne dai alummar kasar Iran ta fara cincirindo akan titunan zuwa masallacin Kudus domin raya ranar Kudus ta duniya.
A nan birnin Tehran manyan jami’an gwamnati ne da su ka hada da shugaban kasa da ministocinsa suke halartar gangami da kuma Zanga-zangar ta raya ranar Kudus.
Bugu da kari babban magatakardar kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Jihadul-Islami, Dr. Ziyad Nakhala yana halarar ranar ta Kudus anan Tehran.
A sauran garuruwa da biranen Iran masu yawa, mutane sun fito kwansu da kwarkwatarsu suna masu bayar da taken yin tir da HKI da kisan kiyashin da take yi wa al’ummar Gaza, haka nan kuma neman a kawo karshen yakin.
Taken da aka bai wa ranar kudus din ta bana shi ne; Guguwar ‘Yan’tattun Duniya” saboda ya dace da farkin “Guguwar Aqsa’ wanda Falasdinawa su ka kai wa HKI.