Iran ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ta shaidawa taron kwance damarar makamai na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva cewa, makaman kare dangi na gwamnatin Isra’ila da suka hada da makaman nukiliya na ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya.
A yayin jawabin da ya yi a ranar Litinin, a babban taro na 2025 kan kwance damara, a hedkwatar MDD dake Geneva, Mr. Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da MDD da su ba da fifiko kan batun kawar da makaman nukiliya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa “dole ne kasashen duniya su tilastawa Isra’ila bin yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi (NPT) don kawar da dukkanin ayyukanta na nukiliya na kasa da kasa.
A yayin da yake bayyana damuwarsa kan barazanar makaman nukiliya da kuma mummunar illar da suke yi ga bil’adama da muhalli, Mr. Araghchi ya yi kira da a sanya makaman nukiliya a kan gaba wajen damuwar kasashen duniya da MDD.
Araghchi ya bayyana irin ayyukan da ba a taba ganin irinsa ba, da suka hada da kisan kare dangi, laifuffukan yaki da laifukan cin zarafin bil Adama da gwamnatin Isra’ila ta aikata a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin lalata yankunan da aka yi wa kawanya tare da mutuwar dubban mutane, musamman mata, yara da kuma tsofaffi.