Iran: Kisan gillar Isra’ila a Gaza tsawon shekara guda ya kara fusata ​​duniyar musulmi

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Esmail Baghaei ya ce shekara guda a jere Haramtacciyar Kasar tana aiwatar da kisan kiyashi a kan al’ummar yankin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Esmail Baghaei ya ce shekara guda a jere Haramtacciyar Kasar tana aiwatar da kisan kiyashi a kan al’ummar yankin zirin Gaza, wanda ya kara  haifar da karin bacin rai a fadin duniyar musulmi.

Baghaei ya bayyana a cikin wani sako da ya aike ta dandalin  X cewa, yakin kisan kare dangi na Isra’ila ya gamsar da dukkanin musulmin duniya cewa ya zama dole a kafa kasar Falastinu mai cikakken ‘yancin cin gashin kai.

A wannan Litinin ce a ka cika shekara guda da Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare da zubar da jini mafi muni a yankin zirin Gaza.

Adadin wadanda suka yi shahada a hukumance ya kai kusan 42,000, yayin da kusan 100,000 suka jikkata, yayin da wasu 10,000 suka bace ba a san makomarsu, wadanda da dama daga cikinsu suna karkashin buraguzai na gine-ginen da Isra’ila ta ruguza a yankin, yayin da kuma akasarin wadanda suka rasa rayukansu ko jikkata mata ne da kananan yara.

Baya ga rayukan da aka rasa, an samu gagarumar matsala a wajen gudanar da ayyukan jin kai a zirin Gaza, inda kusan daukacin mutanen yankin ke fama da karancin abinci da tsaftataccen ruwan sha da magunguna, kamar yadda kuma rahotanni na hukumomin lafiya na kasa da kasa suka tabbatar da cewa yunwa na ci gaba da yaduwa a fadin yankin tare da illata jama’a, kamar dai yadda rahotannin Majalisar Dinkin Duniya suka tabbatar.

Haka nan kuma Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa, hare-haren na Isra’ila sun  raba kashi 90% na mutanen Gaza muhallansu inda suka zama ‘yan gudun hijira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments