Majiyar dakarun IRGC a mashigar ruwa ta Hurmuz ta bada sanarwan konewar jiragen ruwa dauke da man fetur har guda 7 a daren jiya Laraba.
Kamfanindillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran masu kula da mashigar na cewa, da farko akwai jiragen ruwa dauke da mai guda uku da suka yi karo da nakiyoyin ruwa suka fashe kuma suka kamu da wuta suka kone a kudancin mashigar ruwan.
Sannan dakarun sun harba makamai masu linzami kan wasu jirage guda 2 wadanda suke kaurarda mai da suka fito da su daga mashigar ruwa ta Hurmuz zuwa wasu guda biyu. Labarin ya ce dukkan jiragen guda 4 sun kone. Labarin ya kara da cewa dukkan jiragen guda 4 sun sabawa dokokin wucewa da mashigar ruwa ta Hurmuz wanda JMI ta shimfida da sharuddan wucewa da mashigar.