Search
Close this search box.

​Iran: Jagora Ya Shuka Itacen Zaitun A Ranar Dabi’a Don Nuna Goyon Baya Ga Al-Ummar Falasdinu

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan JMI Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae ya shuga itacen zaitun a safiyar yau Talata, a ranar dabi’a ta

Iran-Iran Jagora Ya Shuka Itacen

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan JMI Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae ya shuga itacen zaitun a safiyar yau Talata, a ranar dabi’a ta kasa da kuma bunkasa shukar iytatuwa a kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jagoran a jawabin da ya gabatar bayan shuka itace saboda raya wannan ranar ya bayyana cewa a bikin ranar shuka itatuwa na bana ya zabi shuka itaciyar zaitun ne don girmama al-ummar Falasdinu wadanda suke fuskantar kisan kiyashi a hannun sojojin HKI da magoya bayanta.

A wani bangare na jawabinsa jagoran ya yabawa mutanen kasar Iran saboda fata da suke yi don kada kuri’unsu a zaben majalisar dokoki da na majalisar kwararru masu zaben jagora wadanda aka gudanar a ranar daya ga watan maris da ya shigo.

Ma’aikatar harkokin cikin gida wacce ta ke kula da al-amuran zabubbuka a kasar ta bayyana cewa fiye da kashi 40% na wadanda suka cancanci kada kuri’unsu ne suka kada kuri’inci a zaben na ranar jumma’a kuma fitowar abin yabo ne. Don a cikin mutane miliyon 61.17 wadanda suka hada da mata miliyon 30.22 da kuma maza miliyon 30.94 mutane miliyon 25 ne suka fito don kada kuri’unsu don zaben yan majalisar dokoki 290 da kuma yan majalisar kwararru 88.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments