Iran: Jagora Ya Ce Iran Ba Zata Yi Kasa A Guiwa Ba Wajen Tallafawa Falasdinawa

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar ba zata yi kasa a guiwa ba wajen taimakawa al-ummar Falasdinu a

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar ba zata yi kasa a guiwa ba wajen taimakawa al-ummar Falasdinu a gwagwarmayan da take yi da sojojin HKI.

Shafin yanar gizo na Parstoday ya nakalto jagoran yana Fadar haka a jiya Talata a lokacinda yake ganawa da Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar HAMAS wacce take jagorantar yakin da al-ummar Falasdinu da kawayensu suka shiga da HKI tun kimani watanni 6 da suka gabata.

Jagoran ya kara da cewa jajircewar al-ummar Falasdinu a yakin tufanul Aksa wani al-amari ne wanda ba’a taba ganin irinsa ba, kuma daukaka ce ga addini musulunci.

Sannan ya kara da cewa duk tare da makirce makircen makiya, al-amarin al-ummar Falasdinu ita ce matsalata ta farki na farko, ba kawai cikin al-ummar musulmi da larabawa kadai ba, sai ya ta zama matsala babba ga dukkan kasashen duniya.

A nashi bangaren Isma’ila Haniyya shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas ya fadawa jagoran inda aka kwana a yakin da Falasdinawa da kawayensu suke fafatawa a HKI musamman a Gaza. Ya kuma bayyana cewa yakin Tufanul aksa ta karya HKI har abada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments