Iran Da Saudiyya Suna Tattaunawa Akan Aiki Tare A Fgen Kirkirarriyar Fasaha ( AI)

Mataimakin ministan sadarwa da fasahar tattara bayanai na Iran ne ya sanar da cewa Iran da Saudiyya sun bude tattaunawa akan yadda za su yi

Mataimakin ministan sadarwa da fasahar tattara bayanai na Iran ne ya sanar da cewa Iran da Saudiyya sun bude tattaunawa akan yadda za su yi aikin hadin gwiwa a fagen kirkirarriyar fasaha.

Maitaimakin ministan sadarwar da fasahar tattara bayanai, na Iran Muhammad Muhsin Sadar ya nuna fatansa na ganin an kawo karshen ficewar kwararru zuwa wasu kasashe abinda ake kira da “ Hijirar Kwararru”, idan har ana ba su aiwatar da ayyukan da su ka kware da kuma saukake musayar kwarewa a tsakanin kasashen biyu.

Bugu da kari, Muhammad Muhsin Sadar ya nuna fatansa na ganin cewa an samar da wani yanki na musamman da za a rika samar ayyukan fasaha na koli ( FAVA) na tattara bayanai da musayarsu.

Haka nan kuma ya yi bayani akan yadda ma’aikatar tashi ta kafa asusun musamman na taimakawa masu kirkira a fagen fasaha domin zai samar da ayyuka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments