Iran Da Rasha Zasu Rattaba Hannun Kan Batun Gina Wasu Tashoshin Nukiliya.

Mohammad Eslami mataimakin shugaban kasar Iran kuma shugaban hukumar makamashin nukiliya na kasar Iran ya bayyana cewa Tehran da mosko  za su rattaba hannu kan

Mohammad Eslami mataimakin shugaban kasar Iran kuma shugaban hukumar makamashin nukiliya na kasar Iran ya bayyana cewa Tehran da mosko  za su rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya akwanaki masu zuwa ta gina tashar nukiliya domin kara fadada alakarsu a wannan bangaren na makamashi.

Wannan sanarwar tana zuwa ne adaidai lokacin da iran ke fuskantar matsin lamba kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya ,bayan da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta kasa tabuka komai akan batun.

Karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakani, kasar rasha za ta samar da riaktors guda 8 a cikin iran, hudu daga cikinsu za’a yi amfani da su a tashar ta ta bushahar ne.

Yace an kammala komai game da Tattaunawa da kuma abubuwa da suka shafi kayan aiki, don haka idan aka sanya hannu a wannan mako zaa fara aiki na matakin farko da ya shafi tsari da kuma yadda waje zai kasance.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted