Shugaban rikon kwarya na Iran Mohammad Mokhber ya bayyana alakar kasar da Rasha a matsayin alaka mai tushe da bata canjawa.
Mokhber ya bayyana hakan ne , yayin da yake zantawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho.
Jami’in na Iran ya ce “aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da aka kulla (tsakanin bangarorin biyu) da suka hada da harkokin kasuwanci, zirga-zirga da makamashi, shi ne babban ajandar huldar dake tsakanin kasashen biyu.”
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kuduri aniyar aiwatar da wadannan yarjejeniyoyin, in ji shi.
Mokhber ya ci gaba da yin bitar tsarin hadin gwiwa tsakanin jamhuriyar Musulunci da Rasha , musamman ma game da hanyar zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa, da suka hada sauran yarjeniyoyi na (INSTC), kungiyar kasashe masu tasowa ta BRICS, da kungiyar tattalin arzikin Eurasia (EAEU).
A cikin wannan yanayin , ya ba da fifiko kan karfafa tushen doka na hadin gwiwar Rasha da Iran.