Iran Da Omman Sun Yi Watsi Da Kudaden Fito A Tsakanin Kasashen Biyu, Tare Da Kara Karfafa Ayyukan Jami’an Costom

Gwamnatin JMI da kuma sarakunan kasar Omman sun cimma matsaya ta yin watsi da kudaden fito kan kayakin da kasashen biyu don bunkasa harkokin kasuwanci

Gwamnatin JMI da kuma sarakunan kasar Omman sun cimma matsaya ta yin watsi da kudaden fito kan kayakin da kasashen biyu don bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministocin kasuwanci na kasashen biyu Muhammad atabak da Qais Mohammed al-Yousef suna fadar haka bayan taron kwamitin tattalin arziki na kasashen biyu.

Labarin ya kara da cewa wannan shi ne taron kwamitin tattalin arziki na kasashen biyu wanda aka gudanar a birnin Mascat na kasar Omman.

Ministan harkokin kasuwanci na kasar Iran Muhammad Atabak da tokwaransa na kasar Omman ne suka jagoranci taron kwamitin a wannan karon. Kuma sun agenda taron nasu guda uku ne. Nafarko yin watsi da kudeden fito tsakanin kasashen biyu don bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Na biyu kuma sun tattauna batun karfafa harkokin kasuwanci tsakanin kasashne biyu.

Sai kuma agenda na uku sun karfafa bukatar jami’an kwoston na kasashen biyu su karfafa ayyuka a kan iyakokin kasashen biyu don tabb atarda da cewa wasu basu yi amfani da wannan damar don kai kawo da kayakin da aka haramta sub a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments