Iran Da Najeriya Sun Yi Allwadai Da Harare Ta’addanci A Mosco

A dai dai lokacinda yawan wadanda suka rasa rayukansu a harin ta’addancin da aka kai a kan wani wuri a birnin Mosco ministan harkokin wajen

A dai dai lokacinda yawan wadanda suka rasa rayukansu a harin ta’addancin da aka kai a kan wani wuri a birnin Mosco ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdullahiyan yayi allawadai da hare haren wadanda kungiyar yan ta’adda ta ISIS ta daukik alhakin kaiwa. Ya kuma jajantawa gwamnatin da kuma mutanen kasar Rasha wadanda abin ya shafa.

Har’ila yau a wani bayani wanda ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar ta bayyana jajenta ga gwamnatin kasar Rasha da kuma iyalan wadanda hare haren ta’adancin ya shafa.

Bayanin ya kara da cewa gwamnatin Najeriya tana tare da gwamnatin Rasha a irin wannan hali nab akin ciki sannan tana rokon gafawa wa rayukan da aka rasa da kuma fatan saurin murmurewa ga wadanda suka ji rauni.  

Majiyar hukumar leken asiri ta kasar Rasha  FSB  ta bayyana cewa ta kama mutane 11 kan wannan harin, wadanda kuma suke saurin zuwa kan iyakar kasar da Ukraine. Wasu jami’an gwamnatin kasar Rasha sun nuna yatsun tuhuma kan kasar Ukraine, da kuma kasashen yamma. Amma har yanzun shugaba Putin bai yi wata magana dangane da hare haren ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments