Ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa Iran ta yi azamar aiki tare da kasar China na tsawon shekaru 25 wanda zai zama ginshikin bunkasa fadada alakar tasu a fagage mabanbanta.
A yau Asabar ne dai ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kai ziyara kasar China inda ya gana da takwaransa Wang Yi.
A yayin ganawar, bangarorin biyu sun nuna aniyarsu ta bunkasa alaka mai muhimman a fagagen cigaba a tsakanin kasashensu.
Fagagen da wadanan alakar za ta shafa, sun hada tattalin arziki, kasuwanci, zuba hannun jari, makamashi, da kuma sufuri.
Arakci ya tabo doguwar alakar da take a tsakanin kasashen biyu tun daga tsohon cigaban kasashen biyu a Asiya, sannan ya kara da cewa, Iran tana son amfani da wannan damar domin fadada fagen aiki tare wanda a karkashin wani shiri na shekaru 25.
A nashi gefen, ministar harkokin wajen China ya yi ishara da muhimmancin da Iran take da shi a cikin yammacin Asiya, haka nan kuma albarkatunta na dabi’a, bagiren da take cikinsa da kuma mutanenta. Haka nan kuma ya bayyana aniyar shugabannin kasashen biyu na bunkasa alaka a tsakanin kasashensu. Dangane da abubuwan da suke faruwa a yammacin Asiya kuwa, kasashen biyu sun yi kira da a kawo karshen tsoma bakin kasashen waje, domin barin ‘yan asalin yankin su ayyana makomarsu