Gwamnatocin kasashen China da Iran sun kaddamar da layin dogo na jigilar kayaki tsakanin kasashen biyu da kuma zuwa turai don bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu da kuma kasashen yankin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa layukan dogon guda biyu ne mai zuwa da kuma mai dawowa daga bangarorin biyu.
Kuma daga jiya Lahadi ne jigin daukar kaya na farko daga Iran zuwa chaina zai fara aiki. Sai dai idan an kammala layin dogo daga Rasht – Astana, Zirga zirgan zai hada kasashen turai da Iran da kuma China.
Masana sun bayyana cewa idan aikin ya kamala za’a samu ragin lokaci jigilar kaya a tsakanin kasashen yankin, kuma akwai sauki wajen kudaden jigilar.
Masana suna ganin idan wannan layin dogo ya kama aiki gadan gadan muhimmancin mashigar ruwa ta Suez ta kasar masar zai ragu. Banda haka Iran zata sami nasara karya takunkuman tattalin arzikin da kasashen turai suka dorawa kasar.
Marigayi shugaba Shahid Ra’isi ne ya fara wannan shirin, wanda ya kai ga samun nasara, kuma wannan mataki ne babban na kulla zumunci mai karfi tsakanin kasashen yankin Asia ta kudu da Iran.
Shugaban kasa mai shigowa Mas’ud Pezeshkiya dai ya tabbatar da cewa zai ci gaba da ayyukan da marigayi Ra’isi ya fara a karkashin kungiyar BRICS ko SHANGHAI da sauransu.