Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran Janar Hussain Salami ya bayyana cewa kasar Iran ta rage karfin ikon da kasar Amurka take da shi a duniya a bangarori daban daban a cikin shekarun da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Janar Salami yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a birnin Mashahad da ke arewa maso gabacin kasar Iran a jiya Talata.
Salami ya kara da cewa a cikin shekaru 30 zuwa 40 da suka gabata juyin juya halin musulunci a kasar Iran ya rage karfin kasar Amurka a bangarori da dama, daga ciki har da karfin karfin sojenta.
Ya kuma fara bada misali da mamayar ofishin jakadancin kasar Amurka dake birnin Tehran a cikin watan Nuwamban shekara ta 1979, da kuma yadda Amurka ta kasa kwato jami’an ofishin jakadancin da karfin soje.
Har’ila yau hare haren maida martanin da sojojin Iran suka kai kan sansanin sojojin Amurka da ke Ainul Asad a cikin watan Jenerun shekara ta 2020 ya kaskanta Amurka a duniya.
Banda haka yace, hare haren da ta kai HKI a bayayan nan duk sun sanya duniya ta fihinci cewa karfin Amurka ya ragu a duniya. Har’ila yau kukarinta na ware kasar Iran daga sauran kasashen duniya bai sami nasara ba.
Daga karshe ya kammala da cewa hatta zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar Iran bayan shahadar shugaba Ra’isi, wani ci gaba ne a damocradiyyar addini wanda kasar Iran ta gabatar a matsayin tsarin da yafi democradiyyar Amurka.