Search
Close this search box.

Iran: An kawo karshen yakin neman zaben shugaban kasa zagaye na biyu

Da misalin karfe 8 na safiyar yau Alhamis aka kawo karshen yakin neman zabe na ‘yan takarar shugabancin kasa zagaye na biyu An kammala yakin

Da misalin karfe 8 na safiyar yau Alhamis aka kawo karshen yakin neman zabe na ‘yan takarar shugabancin kasa zagaye na biyu

An kammala yakin neman zaben ‘yan takarar ne a fadin kasar  da karfe 8:00 na safiyar yau Alhamis4 ga watan Yuli.

A bisa dokar zaben, an hana gudanar da duk wani kamfe a cikin sa’o’i 24 kafin a fara zaben.

A ranar Lahadin da ta gabata ce aka fara yakin neman zaben ‘yan takarar zaben shugaban kasa zagaye na biyu, bayan tabbatar da sahihancin zaben a kashi na farko da majalisar tsaro ta yi.

A kashi na biyu na zaben shugaban kasa, an gudanar da muhawara sau biyu ne tare da tattauna batutuwan siyasa, al’adu da tattalin arziki. Har ila yau, an watsa shirye-shiryen ‘yan takarar biyu da kuma hirar da suka yi ta talabijin da jama’a kan tsare-tsaren da suke da su.

A matakin farko na zaben shugaban kasa, wanda aka gudanar a ranar Juma’a 28 ga watan Yuni, Mustafa Pourmohammadi, Saeed Jalili, Mohammad Baqer Qalibaf, da Masoud Pezeshkiyan  su ne suka fafata da juna, amma saboda babu daya daga cikinsu da ya iya lashe mafi rinjayen kuri’u, aka tsawaita zaben zuwa zagaye na biyu , inda Masoud Pezeshkiyan da Saeed Jalili, wadanda suka zo na daya da  na biyua  zaben zagaye na farko za su kara a zagaye na biyu.

A gobe Juma’a 15 ga watan Yuli ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a kashi na biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments