Amir Khrasani wani ba’irane ya rubuta a shafinsa na X kan cewa Amurka tana amfani da HKI a matsayin makami wajen fuskantar kasashen duniya, da kuma jujjuyata kamar yadda take so.
Kharasani ya bayyana hakane a shafinsa na X ya kuma kara da cewa, kamar sauran hanyoyi da take bi na jujjuya al-amura a duniya, kama daga Holywood, kungiyoyin kare hakkin bil’adama, kungiyoyin kasuwanci ta duniya da sauransu, Amurka tana amfani da samuwar HKI a gabas ta tsakiya don jujjuya yankin gabas ta tsakiya da kuma duniyar da ita. Da wannan dalilin ne ba zata taba yanda HKI ta fadi ba.