Iran, ta bakin ministan harkokin kasar, ta bukaci da a yanke duk wata huldar diflomatsiyya da tattalin arziki da Isra’ila da kuma kakaba mata takunkumai saboda kisan kiyashin da take ci gaba da aikatawa kan al’ummar Falasdinu.
Amir Abdolahian, ya bayyana cewa, yadda gwamnatocin kasashen musulmi suka tunkari kisan kare dangi da ake yi wa Falastinawa a zirin Gaza zai kasance a cikin tarihi.
Babban jmai’in diflomatiyyan na Iran, ya bayyana hakan ne a wurin taron kungiyar hadin kan kasashen muuslimi karo na 15 da aka soma jiya Asabar a Banjul, babban birnin kasar Gambia.
Ya kara da cewa dakatar da safarar makamai da kasuwanci da Isra’ila wani muhimmin makami ne na dakatar da kisan kare dangi na Sahayoniyawan a zirin Gaza da kuma mamayar da take a yammacin gabar kogin Jordan da kuma gabashin Quds.
Yayin da yake yin kakkausar suka kan ci gaba da aikata laifukan da ya danganta da na dabbanci da gwamnatin sahyoniyawan ke aikatawa kan al’ummar Gaza, ya jaddada wajabcin karfafa hadin kai tsakanin kasashen Musulmi.
‘’Muna bukatar hadin kai fiye da ko wane lokaci, domin kawo karshen kisan gillar da ake yi nan take, da hada kai da kuma bukatar aikewa da agajin jin kai cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba a duk yankunan Gaza, da kuma janyewar sojojin Isra’ila a Gaza, da tsagaita wuta, inji babban jami’in diflomatisyya na Iran, Hossein Amir Abdolahian a taron na OIC a Gambia.