Iraki: Masu Gwagwarmaya Sun Cilla Makamai Kan Sansanonin Sojojin HKI A Kan Tuddan Golan

Mayakan hashdu ashabi a kasar Iran sun bada sanarwan cilla makamai a kan sansanin sojojin HKI a yankin tuddan Golan na yammacin kasar Siriya wanda

Mayakan hashdu ashabi a kasar Iran sun bada sanarwan cilla makamai a kan sansanin sojojin HKI a yankin tuddan Golan na yammacin kasar Siriya wanda HKI take mamaye da su.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto bayanin da dakarun suka fitar a ranar jumma na cewa sun yi amfani da makamin Dron wato jirgin konan bakin waje wanda ake sarrafashi daga nesa a hare haren na ranar jumma’a.

Kafin haka, kwanaki uku da suka gabata kungiyar ta bayyana cewa ta kai hare hare kan tuddan na Golan a dai dai lokacinda ministan yaki na HKI yake ziyarar aiki a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments