Wani jami’in gwamnatin kasar Iraki ya bayyana cewa, idan gwamnatin HKI ta kuskura ta farwa kasar Leabanon da yaki nag aba daya, dakarun kawancen masu gwagwarmaya zasu fafata da su a kan iyakokin kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abu Alaa Al-walae babban sakatarin rundunar Sayyidushuhadaa na kasar Iraki yana fadar haka.
Dakarun dai suna daga cikin gamayyar dakarun masu fada da ayyukan ta’addanci a kasar Iraki, ta Hashdushaabi, kuma yana daga cikin dakarun gamayyar masu gwagwarmaya a yanking aba daya.
Dakarun Sayyidushuhadaa dai ta fara kai harehare kan HKI tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata kan HKI saboda kisan kiyashin da sojojin ta suke yi a gaza.
Ya zuwa yanzu dai dakaru masu gwagwarmaya a kasar Iraki sukan kai hare hare kan wurare masu muhimmanci a HKI daga nisan kilomita 800.
Alwalae ya kara da cewa dakarun zasu dauke wannan tazarar idan har ta kuskura ta farwa kasar Lebanon da yaki gama gari.