IMF na shirin tattauna batun basussukan da ke kan Senegal

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fada a wannan alhamis cewa yana shirin aikewa da tawaga zuwa kasar Senegal a cikin watan Augusta

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fada a wannan alhamis cewa yana shirin aikewa da tawaga zuwa kasar Senegal a cikin watan Augusta domin tattauna yadda aza magance matsalar basussukan da ke kan kasar  da kuma fara tattaunawa kan tsarin sabon shirin lamuni.

Kasar Senegal na fama da bashin biliyoyin daloli da gwamnatin da ta shude ta karba, lamarin da ya sanya asusun lamuni na duniya IMF ya dakatar da shirin ba da lamuni ga kasar.

A nasa bangaren kuma, wani mai magana da yawun IMF ya ce, “Asusun na bukatar karin bayanai kafin ya karfafa kimanta halin da ake ciki na basussukan kasar Senegal, sannan yana bukatar yarjejeniya kan muhimman matakan gyara.”

Ya kara da cewa, “Da zarar mun cimma matsaya kan manyan matakan gyara, hukumar ta IMF za ta sake yin nazari kan batun, yana mai bayyana cewa “zai yiwu a cimma matsaya kan wadannan matakan nan da makonni masu zuwa.”

Kakakin ya kara da cewa “Hukumar lamuni ta duniya IMF ta yi kiyasi  bisa ga sabbin bayanai daga hukumomin kasar Senegal cewa basusukan da aka boye wanda gwamnatin da ta gabata ta karb, sun kai dala biliyan 11.3 a karshen shekarar 2023. Wannan ya hada da wani kaso na bashin kamfanonin gwamnati da aka kiyasta kusan kashi 7.4% na GDP.”

Kakakin IMF ya ce zai ba da bayanai ga hukumar kan yadda lamarin ya faru , yana mai cewa “IMF na gudanar da bincike na cikin gida da tantancewa a matsayin wani bangare na rashin bayar da rahotonni da suka dace.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted