IAEA : Grossi Na Fatan Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya bayyana fatansa na ganin an farfado da yarjejeniyar nukuliyar Iran. Rafael Grossi, ya yi

Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya bayyana fatansa na ganin an farfado da yarjejeniyar nukuliyar Iran.

Rafael Grossi, ya yi wanan tsokacin ne a matsayin amsa ga bukatar sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, wanda son a sabunta tattaunawa da nufin samun fahimtar juna game da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.

Ya bayyana fatan cewa za a farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran, da nufin tabbatar da zaman lafiya na ayyukan nukiliyar Iran.

Rafael Grossi, a wata hira da ya yi da tashar Al-Arabiya, ya ambaci shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya, ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda kasar ke ci gaba da tara sinadarin uranium da ta inganta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments