Human Rights Watch: Kashin 72% Na Al’ummar Duniya Suna Rayuwa Karkashin Gwamnatocin Kama-Karya

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Right Watch ta ce: Kashi 72% na al’ummar duniya suna rayuwa ne a karkashin gwamnatocin kama-karya Kungiyar kare

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Right Watch ta ce: Kashi 72% na al’ummar duniya suna rayuwa ne a karkashin gwamnatocin kama-karya

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta yi gargadin a cikin rahotonta na shekara-shekara da ta fitar ranar Laraba cewa: Kare hakkin dan adam yana cikin babban hatsari, musamman a karkashin matsin lambar Shugaban Amurka Donald Trump, tana mai da’awar cewa “karya tasirin mulkin kama-karya a duniya” shine kalubalen zamaninmu.

A cikin rahotonta, wanda ya shafi abubuwan da suka faru har zuwa shekara ta 2025, kungiyar kare hakkin dan adam ta jaddada cewa: Kashi 72% na al’ummar duniya suna rayuwa ne a karkashin gwamnatocin kama-karya, wanda hakan ya mayar da matakan dimokuradiyya zuwa yadda suke a shekarar 1982.

“Rahoton Duniya na shekara ta 2026” na kungiyar mai shafuka 529 ya sa ido kan ayyukan kare hakkin dan adam a kasashe sama da 100, ciki har da Amurka, China, Rasha, Haramtacciyar kasar Isra’ila, Indiya, Iran, da wasu kasashen Larabawa da dama.

Kungiyar Human Rights Watch ta yi gargadin cewa: Tsarin kare hakkin dan adam yana fuskantar barazanar rugujewa yayin da take hakkin dan adam ke kara ta’azzara a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments