Saudia Ta ce Hare Hare Kan Riyar Ya Kashe Mutane 12i

Mutane 12 suka mutu sanan wasu 300 suka ji rauni sanadiyyar hare haren da mayakan Yemen suka kai kan tashar jiragen sama na Sarki Khalid

Mutane 12 suka mutu sanan wasu 300 suka ji rauni sanadiyyar hare haren da mayakan Yemen suka kai kan tashar jiragen sama na Sarki Khalid ta kasa da kasa da ke birnin Riyad babban birnin kasar Saudia.

Shafin yanar gizo na Arabnews ya nakalto hukumar zirga zirgan jiragen sama na kasar  saudia tana fadar haka a jiya Asabar.

Labarin ya kara da cewa hare haren da mayakan Yemen ya bar wasu mutane 309 da raunuka daban daban.

 A dai dai lokacinda yaki yake kara zafi tsakanin Mayakan Yemen wadanda suke samun nasarar korar sojojin hayan kasar Saudia a kasar Yemen, yakin yana zawo zubar da jinni a bangarorin biyu.

Wasu kafafen yada labaran sun bayyana cewa jiragen yakin saudia sun kai hare hare da jiragen sama kan yankunan da dama a kasar Yemen a jiyan inda suma suka kashe daruruwan fararen hula.

Huthawa sun kwace babun mandab da yankunan da dama daga hannun sojojin hayar Saudi a kudancin Yemen. Ansarullah sun ce ba zasu daina yakin ba sai saudia ta dauke mata takunkuma tattalin arzikin da ta dorawa kasar shekaru 12 da suka gabat sannan ta fice daga kudancin kasar da ta mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted