Hukumar UNRWA Ta Ce; Akwai Barazanar Bullar Ambaliyar Ruwa A Yankin Zirin Gaza

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta ce: Falasdinawa rabin miliyan a Gaza na cikin hadarin fuskantar ambaliyar ruwa

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta ce: Falasdinawa rabin miliyan a Gaza na cikin hadarin fuskantar ambaliyar ruwa

Mai magana da yawun hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ta jaddada cewa: Kusan rabin al’ummar Gaza na cikin hadarin fuskantar nutsewa cikin ruwan sama sakamakon ambaliyar da zata faru a yankin.

Jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya ta ruwaito daga mai magana da yawun hukumar ta UNRWA tana cewa: Mutane rabin miliyan a Gaza na cikin hadarin ambaliya da zarar ruwan sama ya sauko a yankin.

Kakakin ta kara da cewa: An kwashe watanni 6 ana dakatar da motocin dakon kaya 33 dauke da katifu a kusa da kan iyaka da Masar saboda takunkumin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kakaba musu.

Mai magana da yawun Hukumar ta UNRWA ta yi nuni da cewa: Mazauna Gaza da ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki suna fuskantar ƙarin haɗarin cututtuka a lokacin damuna da sanyi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments