Hukuma mai kula da al-amuran sadarwa ta Najerira wato ‘The Nigerian Communications Commission (NCC) ya bada sanarwan cewa, ta amincewa kamfanonin sadarwa na wayoyin tafi da gidanka, su kara kudadi a kan irin khidimomin da suke yiwa masu amfani da wayoyin hannu a kasar.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta kara da cerwa, kamfanonin sun dade suna matsawa hukumar kan ta amince masu kara wani abu daga cikin ayyukan da suke yuwa masu wayayin hannu, kamar kira da kuma aika sakunni a rubuce , da internet da sauransu.
Wani jami’in hukumar ya fadawa Premium times kan cewa, a halin yanzu hukumar ta amincewa kungiyar kamfanonin sadarwa na kasar, wato (Telcos) yin hakan bisa sanya ido na hukumar ta NCC.
Wasu wadanda suka kan al-amuran sun bayyana cewa kamfanonin sadarwa a Najeriya suna amfani da lita miliyon 40 ba man desel don tafiyar da ayyukansu, wanda ba zai ci gaba da kasancewa haka ba, da wannan tsadar da man desel yake yi a kasar.