Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ya bayyana cewa, tare da himma da kuma jajircewar hukumarsa, ta sami nasar kauda tasirin takunkuman da kasashen yamma suka dorawa hukumarsa.
Kamfanin dillancin labaran Sahab ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran, ya na cewa, jajircewar kasar Iran a kan takunkuman da kasashen yamma, musamman Amurka suka dorawa hukumar makamashin nukliya na kasar, ya sa sun sami nasarar bata tasirin takunkuman a kan hukumar, don duk abinda suke son Iran kada ta samu, tare da wadannan takunkuman, ta samu.
Muhammad Islami ya kara da cewa a ranar 31 na watan Decemban 2024 da muke ciki ne hukumar baitul malin kasar Amurka ta dorawa wani karamin sashe a hukumarsa takunkumi, da kuma haramcin samun wasu bukatunsa.
Don haka ba wani tasirin da takunkumin zai yi, a aikin wannan sashen saboda, baata bukatar wadannan abubuwan daga Amurka ko wata kasar waje.