Majiyar hukumar fursinoni ta Falasdinawa ta bada sanarwan cewa a gaggauta ceto fursinoni daga yankin Gaza wadanda gwamnatin mamaye take tsare da su a gidan yarin Arramlah da gaggawa saboda suna cikin mummunan hali.
Ofishin hukumar Fursinonin ta bada sanarwan ne a safiyar yau Alhamis ta kuma kara da cewa, hukumomin gidan yari a Arramlah suna azabtar da falasdinawa da ke hannunsu, azaba mai tsanani wanda yake da muni sosai.
Labarin ya kara da cewa, hukumomin gidan yarin suna barazana ga fursunonin kan cewa idan sun kuskura sun bayyana halin da suke ci ga masu ziyarar zasu kara yawan azabtarwa da suke masu. Labarin ya nakalto wasu fursunonin na karafin yadda ma’aikatan gidan yarin suke daure idanunsu na lokaci mai tsawo da rana da kuma rashin sanin lokacin buda baki da kuma sahur a cikin azumi saboda babu mai agogo a cikinsu.
Hukumar ta dorawa hukumomin gidajen yarin HKI laifin duk abinda ya sami wadan nan fursunoni, sannan ta yi kira ga kungiyar red Cross ta kasa da kasa ta gaggauta yin wani abu kafin wadan nan yahudawa su gurgunta rayuwar wadanan falasdinawa daga gaza.