Hukumar Alhazai Ta Kasa A Nigeriya Ta sanar Da Rage Kudin Farashin Aikin Hajji Na Bana

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da yadda aikin hajjin bana zai kasance dangane da abin da ya shafi kudin kujerar aikin da

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da yadda aikin hajjin bana zai kasance dangane da abin da ya shafi kudin kujerar aikin da lokacin da za a rufe karbar kudin maniyyata.

Wannan dai ya biyo bayan kulla yarjejeniyar gudanar da aikin Hajji ta 2026 da hukumar ta yi a madadin Najeriya da hukumomin kasar Saudiyya, a lokacin wani biki da aka gudanar a birnin Jeddah na Saudiyya.

Shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin ministan Hajji na Saudiyya Abdulfatah Mashat ya wakilci Saudiyyar.

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da rage kudin kujerar aikin hajji ne, bisa umarnin shugaban ƙasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments