Jagoran kungiyar Ansarullah da aka fisani da ta ‘yan Houthi a Yemen, ya sake jaddada goyon bayan kasar ga Falasdinawa wadanda ke fuskantar yakin kisan kiyashin Isra’ila.
Abdul-Malik al-Houthi ya bayyana hakan ne a bikin da aka gudanar a ranar Lahadin na Maulidin Annabi Muhammad (SAW) a birnin Sana’a inda dubban ‘yan kasar Yemen suka taru.
Ya ce harin makami mai linzami na baya-bayan nan da Yemen ta kai, wani bangare ne na ci gaba da kai hari kan Isra’ila.
Houthi ya jaddada cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan kyamar Isra’ila har sai gwamnatin ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi a zirin Gaza da kuma killace yankin.
Zamu ci gaba da tsaya tsayin daka har sai an tsarkake Falasdinu daga kangin mamayar,” inji shi.