Isra’ila Ta Rusa Gidajen Falasdinawa Fiye 11,000 A Qudus Da Wasu

Wata kungiyar kara hakkin bil’adama ta Falasdinawa  ta bada sanarwan cewa, sojojin HKI sun rusa gine ginen Falasdinawa wadanda suka hada da gidajen zama da

Wata kungiyar kara hakkin bil’adama ta Falasdinawa  ta bada sanarwan cewa, sojojin HKI sun rusa gine ginen Falasdinawa wadanda suka hada da gidajen zama da kuma shaguwa gonaki da wuraren sana’o’insu har 11,620 a cikin shekaru 3 da suka gabata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar na cewa tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne sojojin yahudawan suka fara wani shiri na musamman don korar falasdinawa daga yankin yamma da kogin Jordan a dai dai lokacinda suke fara kisan kiya shi a gaza.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Falasdinawa (MOATA) ta cewa HKI ta rusa gine gine ne a yankin yamma da Kogin Jordan da kuma birnin Qudus, wanda ya hada da gidajen zama 2,143 sai kuma sauran gine gine wadanda suka hada da shaguna, gonaki, wuraren sana’o’I da kamfanoni da sauransu. Wannan yana faruwa tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.

Labarin ya kara da cewa hukumar kare hakkin bil’adama na MDD tun wannan lokacin sun tilastawa wasu falasdinawa a sansanonin yan gudan hijiran da ke yankin barin wurarensu, daga ranar 4  ga watan satumban shekara ta 2025. Kuma take amincewa su koma gidajensu har yanzun. Kuma wuraren sun hada da sansanonin yan gudun hijira na Jenin Tulkaram da kuma Nur Shams. Kuma sun lalata mutane da wasu ababen hawa na falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted