Majiyoyin gwamnatin HKI sun bayyana cewa sun kama wani bayahude soja yana aiki wa kasar Iran, musamman a cikin yakin kwanaki 12 da suka fafata da JMI.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar yahudawan na cewa a jiya Alhamis ne aka gurfanar da sojan a gaban kotu a karo na farko tare da tuhumarsa da aika wasu bayanai zuwa wani ma’aikaci a kasashen waje. Kuma abubuwan da ya aika sun hada da hotunan Bidiyo na inda makamai masu linzami n a kasar Iran suka fadi da kuma na garkuwan makaman masu linzami, su kuma yadda suke kakkabo makaman kasar Iran a cikin yakin kwanaki 12.
A wani lokaci a cikin yakin gwamnatin HKI ta haramta aika hotunan abubuwan da ke faruwa a yakin ga wani musamman a kasashen waje.
Labarin ya kara da cewa za’a ci gaba da tsare sojan zuwa ranar talata mai zuwa. Majiyar ta ce sojan dan shekara 33 a duniya, wanda ba’a bayyana sunansa ya dauki hotunan tun ana yakin kuma yayo kokarin aika wadanda hotuna ga wani ba’irane a wajen kasar sannan shi kuma su bashi kudade.