Search
Close this search box.

HKI Ta Kama Falasdinawa Kimani 9,600 Daga Watan Octoban Da Ya Gabata Zuwa Yau

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Falasdinawa ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kama falasdinawa kimani 9,600 tun daga ranar 7 ga watan Octoban

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Falasdinawa ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kama falasdinawa kimani 9,600 tun daga ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata ya zuwa yanzu.

Hukuma mai kula da Falasdinawa Fursinoni da kuma wadanda ake tsare dasu tare da hadin giwa da wasu kungiyoyin sun tabbatar da cewa sojojin yahudawa a yankin yamma da kogin jordan kadai sun kama Falasdinawa mata 325, yara 670 sannan yan jarida 88 suna ci gaba da tsare su a wurare daban daban a cikin kasar.

Labarin ya kara da cewa a cikin wannan lokaci gwamnatin HKI ta fidda sammacin kama Falasdinawa ko kuma tsawaita tsarewansu har guda 7,500 daga watan Octoba zuwa yanzu.

HKI ta samar da wata doka wacce take kira ‘tsarewar gudanar’ doka wanda yake basu damar kamawa da kuma tsare Falasdinawa ba tare da gabatar da su a gaban kotun ba har zuwa tsawon lokacin da su ka ga dama.

Rahoton ya kammala da cewa sojojin yahudawan suna azabtar da Falasdinawan da suke tsare da su sannan da dama daga cikinsu sun kai ga rasa rayukansu ko kuma shahada a gidajenn yarin da ake tsare da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments