Gwamnatin HKI ta kai farmaki kan tawaga masu rajin kare hakkin bil’adama dauke da kayakin agaji a cikin jirgin ruwa dauke da kayakin agaji zuwa zirin Gaza wacce ta hana shigar abinci cikinsa kimani watanni biyu da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar gwamnatin tsibirin Malta na cewa HKI ta kai hari kan jirgin agajin ne tare da amfani da jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga Nesa, a ruwayen kasa da kasa.
Labarin ya kara da cewa jirgin agajin ya tashi daga tsibirin Malta da nufin isa Gaza, saboda isar da kayakin agajin da suke dauke da su zuwa Gaza, wacce aka killace. Yahudawan saun kai hari da misalign karfe 12.23 a lokacin Malta a daren Jumma’a.
Labarin ya kara da cewa ba wanda ya mutu ko ya ji rauni daga cikin wadanda suke cikin jirgin. Kungiyoyin agaji na kasa da kasa ne suka shirya wannan tafiya mai hatsari don tallafawa mutanen Gaza, sannan akwai fitattun mutane a duniya wadanda suke cikin jirgin agajin.
Kungiyoyin sun bukaci a ya All..wadai da HKI, saboda kai wannan harin, sannan a yi allawadai da ita saboda killace yankin gaza da kuma kashe falasdinawa fararen hula maza da mata.