Ministan harkokin wajen HKI, Israel Katz, ya bada sanarwan cewa gwamnatin haramtacciyar kasar ta sha alwashin fidda falasdiwa daga yankin yamma da kogoin Jordan musamman daga arewacin yankin, saboda a binda ya kira tungar yan ta’adda wanda falasdinawa suka kafa a yankin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Katz yana fadar haka a shafinsa na X a yau Laraba bayan da sojojin HKI suka kashe falasdinawa akalla 11 a yankin arwacin yamma da kogin Jordan.
Katz ya kara da cewa sansanonin yan gudun hijira wadanda suka hada da Jenin, Tulkaram, Tubas duk suna daga cikin inda za’a aiwatar da shirin korar Falasdinawan.
Kafin haka dai sojojin HKI sun kori Falasdinawa a yankuna daban daban a Gaza ba sau guda ba, wanda kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa da kuma kotun ICC duk suka tabbatar da cewa hakan aikata laifin yaki ne a bisa dokokin kasa da kasa.