Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa tun da aka kafa rundunar Golani a 1948 ba ta taba fuskantar asara kamar wacce a yanzu take gani ba a kudancin Lebanon.
Tsohon mataimakin kwamandan rundunar Golani Yuali Aur, ne ya bayyana haka a jiya Alhamis bayan da mayakan kungiyar Hizbullah su ka kashe sojojin mamaya 5 da kuma wani kwamanda a bugu daya.
Majiyar Hizbullah ta ce, makiya suna rage hakikanin asarar da suke fuskanta a filin daga saboda ba su fadin yawan sojojinsu da ake kashewa.
Tashar talabijin din ta 12 ta HKI ta bayyana cewa; Binciken farko yana nuni da cewa an kashe sojojin ne a cikin wani gida da su ka shiga sannan mayakan Hizbullah su ka fito su ka kai musu hari.
Tsohon mataimakin rununar ta Golani ya yi ishara da yawan kashe sojojin wannan runduna da mayakan kungiyar Hizbullah suke yi, tare da cewa, tun da aka kirkiri rundunar ba su taba fuskantar asara kamar a wannan lokacin ba.
Kusan wata daya da rabi kenan rundunonin sojan HKI suna kokarin kutsawa cikin kudancin Lebanon a kasa, amma sun kasa saboda yadda suke fuskantar turjiya mai tsanani daga mayakan Hizbullah.