Kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta fitar da sanarwa a jiya Alhamis tana mai gargadi akan kin ficewar sojojin HKI daga kudancin Lebanon bayan cikar kwanaki 60 daga dakatar da yaki, kamar yadda ya zo a cikin yarjejeniyar da aka cimmawa.
Sanarwar ta kungiyar Hizbullah ta ci gaba da cewa wasu bayanai da suke fitowa masu nuni da akan cewa abokan gaba za su jinkirta ficewarsu daga Lebanon, yana da bukatar dukkanin bangarorin siyasar kasar da su dauki matakin matsin lamba akan wadanda su ka sanya idanu akan yarjejeniyar,domin ganin an cika aiki da ita.
Bugu da kari sanarwar ta ce, duk wani kara lokaci bayan cikar kwanaki 60, to yana nufin keta hurumin kasar Lebano, da kuma shiga wani sabon fasali na mamaya.
Hizbullah ta ci gaba da cewa, tana bin diddigin abubuwan da suke faruwa, kuma duk wani kokarin ci gaba da zaman ‘yan mamaya a Lebanon abu ne da ba za a laminta da shi ba.
A cikin kwanakin nan dai kafafen watsa labarun HKI suna ambaton cewa sojojinsu ba su da shirin ficewa daga kudancin Lebanon a lokacin da aka tsara, za su ci gaba da zama har illa masha Allahu.
Tashar talabijin ta 14; ta ‘yan mamaya ta ambato majalisar HKI tana cewa, sojojin da suke kudancin Lebanon za su ci gaba da zama.