Sabon Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce kungiyar za ta ci gaba da tsayin daka wajen tinkarar ta’addancin Isra’ila kuma ta kuduri aniyar tilastawa Isra’ilar kawo karshen yakin da take yi da Lebanon.
A yayin jawabinsa na biyu tun bayan nada shi a matsayin babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa, kungiyar ba ta dogara da manufofin siyasa na kawo karshen rikicin ba.
Ta haka ne ya tabbatar da cewa tun a yakin Yulin 2006 kungiyar ta shirya tunkarar irin wannan arangama, ta hanyar inganta horo da kuma yadda take gudanar da ayyukanta.
Naim Qasem ya ce yunkurin da Isra’ila ke yi na fatattakar Hizbullah da mamaye kasar Labanon ba zai yi nasara ba saboda tsayin dakan da kungiyar ta yi na kare kasarta.
Shehun ya kara da cewa tushen duk wata tattaunawa na tsagaita bude wuta shi ne dakatar da wuce gona da iri da kuma tabbatar da cikakken kare ikon kasar Labanon.
Sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem, ya bayyana hakan ne yau Laraba yayin bikin cika kwanaki Arbaeen na shahadar Sayyed Hassan Nasrallah.
Ya bayyana mirigayi Sayyed Nasrallah a matsayin wata alama ta musamman ta tsayin daka.